Barkwanci a Ƙasar Hausa: Bitar Asalinsa Da Gurbinsa a Zamantakewar Hausawa

    Tsakure: 

    Wannan nazari an aiwatar da shi ne a kan barkwanci a tsakanin al’ummar Hausawa. Nazarin an aiwatar da shi ne ta hanyar samo bayanai daga litattafai da kundaye da kuma kafafen sada zumunta kamar facebook da TikTok. An gudanar da wannan takarda ta bin bayanan da masani Gusau, (2003) ya kawo na aiwatar da waƙar baka da sauran matanin adabi, an kuma yi amfani da matakan da ra’in ya samar na nazarin waƙar baka da sauran dabarun jawo hankali. Manufar wannan takarda shi ne gano barkwancin da Hausawa suke yi, ta hanyar kafa hujjoji daga bayanan da aka samo daga kundaye da kafafen sadarwa. Sannan an yi sharhin dukkannin abubuwan da nazarin ya gano. A ƙarshe dai binciken ya gano barkwanci, ta hanyar fayyace yadda ake aiwata da shi daki-daki da misalai.

    Fitilun Kalmomi: Barkwanci, Zamantakewa, Asalin Barkwanci

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.007

    author/Gambo, H., Mohammed, S. & Usman, M.I.

    journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |