Tsakure:
Manufar wannan muƙala ita ce nazarin musanya sautukan Hausa waɗanda masu lalurar shanyewar laka (celebral palsy) suke yi. An yi amfani da ra’in ɗabi’antaka (cognitive behavioural theory) da kuma nau’in bincike bi-kwasi (quasi qualitative design) wajen aiwatar da binciken. Muƙalar ta gano masu wannan lalura suna musanya sautukan Hausa a lokacin da suke magana, saɓanin yadda masu cikakkiyar lafiya suke yi. Ta haka ne aka keɓe masu wannan lalura su goma sha biyar (15) na wani lokaci domin ganin sun inganta harshensu ta hanyar gyara waɗannan kurakurai. Muƙalar ta gano daga cikin adadin samfuri 15 da aka keɓe, an samu masu wannan lalura su huɗu (04) waɗanda ba su iya yin magana kwata-kwata a sakamakon yanayin lalurar ta yi masu tsanani. Haka kuma muƙalar ta gano akwai kurakuran musanya sauti da masu wannan lalura suke yi a cikin kalmomi masu gaɓa biyu da masu uku da kuma masu gaɓa huɗu. An kuma samu kurakuran musanya sauti na baƙaƙe guda (75) daga cikin kalmomin da aka taskace, inda aka samu nasarar gyara (39). Haka kuma an gano ɗaukacin masu wannan lalura ba su iya furta waɗannan sautuka /ƙ/ da /ƙw/da /sh/ da /ts/ a sakamakon tawayar harshe da suke da ita. Har ila yau, masu wannan lalura za su iya farfaɗowa da harshensu idan aka ba su kyakkyawar kulawa ta la’akari da lalurarsu. Daga bisani muƙalar ta gano masu wannan lalura ta sahanyewar laka da aka yi gwaji da su, an haife su ne da wannan lalura.
Fitilun Kalmomi: Gaɓar kalma, Lalurar Magana, Musayar Sauti, Shanyewar Laka, Tawayar Harshe
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.008
author/Anas Sa’idu Muhammad & Ashafa Garba
journal/Tasambo JLLC 4(2) | July 2025 |