Tsakure: Al’ada Balarabar kalma ce da a sakamakon zamantakewa ko
saduwar Balarabe da Bahaushe ta samu a harshen Hausa. Al’adunmu sun samu sauyi daga addinan da suka riski ƙasarmu guda biyu (Kiristanci da
Musulunci). Haka kuma, sun gurɓace sanaddiyar Mulkin Mallaka da karatun Boko. Wayewar kan zamani na
hanyoyin sadarwa na baka da rubutattu sun sa masassara ga al’adunmu. Cigaban mai ginar rijiya na hanyoyin sadarwa na ga-ni-ga-ka
na rediyo mai hoto da finafinai, da wasannin kece raini da batsa sun yi wa
al’adunmu rauni babba. Shirye-shirye da tsare-tsaren wayoyin hannu sun mayar da
gaba baya; sun gurɓatar da
kyawawan al’adunmu, muka koma gaba kallo baya da mamaki. Babban abin da ya
kyautata al’adunmu na gado shi ne “gaskiya” abin da ya gurɓatar da su shi ne “ƙarya”. Ga alama, dabarar da muka
fara yi ta leƙon al’adunmu na shekaranjiya, da shekaranjiya ban da jiya, domin gyara su
a yau domin amfaninmu jibi da gata, su ne kaɗai dabarun gyaran gurɓatacciyar al’ada da inganta ta.
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.002
author/Aliyu Muhammadu Bunza
journal/Tasambo JLLC 4(1) | May 2025 |