Hanya Mai Haɗa Zumuntar Dole: Tsokaci Kan Dangantakar Sana’ar Jima da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa

    Tsakure: Dangantaka a tsakanini sana’o’in gargajiyar Hausawa alaƙa ce da ta haɗa sana’o’in ta fuskoki da dama musamman ta yadda suke gudana da kuma yadda hakan yake taimakawa wajen motsa da tafiyar da tattalin arziƙin al’umma. Cikas ga irin waɗannan alaƙoƙin da ke tsakanin sana’o’in Hausawa musamman na gargajiya kan iya durƙushe ko hana gudanuwar wasu sana’oi’in, wanda hakan kan iya haifar da masassara ta tattalin arziƙin al’umma. Babbar manufar wannan muƙala ita ce a yi duba tare da nazarin dangantakar da ke tsakanin sana’o’oin gargajiyar Hausawa da kuma yadda hakan yake taimaka masu wajen biyan buƙatun al’umma. Fito tare da nazarin dangantakar shi zai bayar da damar fahimatar yadda kowace sana’a take dogarau da wasu wajen aiwartar da aikace-aikacenta na yau da kullum. An yi amfani da hanyoyi da yawa wajen tattaro bayanan da suka taimaka wajen rubuta wannan muƙalar da suka haɗa da hirarraki da masu gudanar sana’o’in gargajiya daban-daban. Haka kuma, an tuntuɓi masana, musamman masana al’adu da tattalin arziƙi. Har wa yau, an nazarce rubuce-rubucen da wasu masana suka yi a kan sana’o’in gargajiyar Hausawa. An aza muƙalar a bisa ra’in Alfanun Sassan Al’ada (Functionalism Theory of Culture) don fayyace batutuwan da binciken ya ƙunsa. A ƙarshe, sakamakon binciken ya nuna yadda sana’o’in gargajiya suke tamkar jini da tsoka a tsakankaninsu.

    Fitilun Kalmomi: Dangantaka, sana’o’i, gargajiya

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.003

    author/Dr. Aminu Ibrahim

    journal/Tasambo JLLC 4(1) | May 2025 |