Danganatakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe: Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam

    Tsakure: 

    Ilimin hikimomin al’umma fage ne da ake nazarin tarihin tsofaffin kayan kimiyyar al’umma masu alaƙa da cigaban ɗanadam. ilimin hikimomin al’umma ya ƙunshi rassa da dama da suka haɗa da karin magana da tatsuniya da labarai da da waƙoƙi da sauran fasahar baka na al’ada. Kowane reshe daga cikin rassan nan da aka ambata yana cin gashin kansa ne tare da isar da wani saƙo na musamman ga al’ummar da ta ƙirƙire shi. Yanayin zamantakewa na iya haifar da matsaloli mabambanta cikin al’umma da shafi ɗabi’a ko addini ko tarbiyya ko al’ada da dai sauran su waɗanda idan aka ƙyale su sakaka za su iya kawo taɓarɓarewar zaman lafiya a cikin al’umma. Bugu da ƙari, ilimin hikimomin al’umma na kan samar da nishaɗi da shaƙatawa da kuma hanyoyin kiyayewa da faɗaɗa harshen da ɗabi’un al’umma. Imam a littafinsa na Magana Jari Ce na 1 zuwa na 3, ya yi amfani da karin magana a matsayin kanun ɗiyan labaransa wajen gina labaran da suka dace waɗannan karin magana domin cimma burin manufofin ilimin hikimomin al’umma da aka ambata a sama. Wannan maƙala mai taken ‘Dangantakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe, Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam’ maƙalace da ta fito da dabarun da mawallafin ya nuna yadda Bahaushe yake amfani da karin magana wajen gyara ɗabi’un al’umma da kawo masalaha a duk inda yanayin zamantakewa yake nema ya ɓaci. Maƙalar ta tsakuro wasu ɓangarorin labaran ta kafa hujja da su a matsayin misalan manufarta. 

    Fitilun Kalmomi: Karin Magana, Tunani, Hausawa, Magana Jari Ce

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i02.002

    author/Usman, Muhammad Ph.D.

    journal/Tasambo JLLC 5(2) | February 2026 |