Tsakure:
Wannan takarda ta yi nazari a kan yadda Maguzawan Ƙasar Katsina suke gudanar da sana’ar noma ta hanyar yin wasu dabaru waɗanda suka gada iyaye da kakanni domin samun amfanin gona mai yawa (auki) ba tare da an sanya takin zamani ba. Amfani da tsaraka hanya ce ta samun amfanin gona mai yawa wadda take taimakon Bamaguje ya shahara tare da yin fice a fagen noma da nuna iyawa da ƙwarewa a tsafin noma. Maguzawa suna yin tsafi ne domin bauta ta gida ko zuriya da neman biyan bukatar rayuwa domin ɗorewar gado da samun yarda ga iskoki. Haka kuma, hanya ce ta neman suna da sarautar noma da buwaya da biyan bukata. Bayanan da aka yi amfani da su a wannan bincike, an same su ne kai tsaye daga Maguzawan Ƙasar Katsina ta hanyar tattaunawa da su, tare da ziyartar wasu daga garuruwansu da zantawa da maƙwabtansu dangane da dabarun nomansu. Bayanan da aka samu, sun tabbatar da wanzuwar yin amfani da tsaraka cikin noman nasu har yanzu, duk da yake akwai takin zamani wanda ake zubawa a ƙasa da kuma wanda ake yi na feshi a zamanace. Binciken ya gano ana yin amfani da dabarun tsafin da aka gada wurin iyaye da kakanni (tsaraka) domin a yi fice, samun amfanin gona mai yawa, neman suna, samun abin duniya da kuma yin amfani da wannan hanya ga Hausawa Musulmi, wato an shigo da wasu waɗanda ba su da hurumi cikin al’adun ta fuskan aiwatarwa da amfani da tsafi. To sai dai, tsarakar da Bamaguje ya sanya a gonarsa, ba ta taɓa zama iri guda da wadda ya ba wani wanda ba yanayin tuninin iri guda ba, amma dai ana ganin fa’ida bakin gwargwado fiye da dogaro da sanya takin zamani.
Tubalan Take: Tsaraka, Noma, Maguzawa, Magunguna
DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i02.001
author/Dr. Alamuna Nuhu & Dr. Umar Dauda Waziri
journal/Tasambo JLLC 5(2) | February 2026 |




