Salon Sarrafa Nassi a Adabin Kasuwar Kano: Lalube Cikin Labarin Mace Mutum Na Rahma A. Majid

    Tsakure: 

    Mata marubuta labarai musamman na Adabin Kasuwar Kano suna baza hikimomi da balaga wajen zayyana matsalolin mata don a fahimta sosai. Sarrafa nassi daga ayoyi da hadisai suna cikin abin da suke amfani da su don ankarar da mutane. Labarin Mace Mutum na Rahma A. Majid yana daga cikin labaran da aka yi amfani da wannan salo don gyara martabar mata a idon al’umma. Manufar wannan nazari ita ce, fito da yadda Rahma A. Majid ta sarrafa nasosin Alƙur’ani mai girma da hadisan Manzo SAW don neman ‘yancin mata ta nuna cewa addini bai tauye ‘yancin mata. Dalilin wannan bincike kuwa shi ne, an yi ta nazarce-nazarce kan salon sarrafa nassi a waƙoƙin baka na Hausa amma ba a ci karo da wani bincike da aka gudanar a litattafan Adabin Kasuwar Kano da ya fito da wannan salon a sarrafa nassi ba. Kuma ga shi marubutan sukan yi amfani da irin wannan salo wajen warware jigogin labaransu. Shi ya sa aka ga ya dace a samar da shi don nuna cewa mata ma ba a bar su a baya ba wajen yaɗa manufofin da suka shafi al’umma ta fuskar addini. Haka kuma, don a nuna irin gudummawar da mata marubuta suke ba da wa wajen kawo ci gaban mata ‘yan’uwansu. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike sun haɗa da nazarin ƙwaƙwaf, inda aka yi nazarin littafin Mace Mutum don lalubo nasosin Alƙur’ani da hadisi. Sannan an bibiyi Alƙur’ani mai tsarki don tabbatar da dacewar abin da marubuciyar ta kawo da ayoyin. An ɗora wannan bincike kan hanyar nazari da amfani nassi wadda Bunza (2009) ya assasa. Binciken ya gano cewa Rahma A. Majid ta yi amfani nassosin Alƙur’ani da Hadisi a cikin labarin Mace Mutum domin kafa hujja da kare martabar mata.

    Keɓaɓɓun Kalmomi: Salo, Nassi, Adabin Kasuwar Kano, Mace Mutum, Rahma A. Majid

    DOI: www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i02.004

    author/Zainab Isah PhD

    journal/Tasambo JLLC 5(2) | February 2026 |